Halinmu ne ya kayar da mu — PDP

Tambarin Jam'iyyar PDP
Image caption Ko a kwanakin da suka wuce sai da aka samu rikicin shugabanci a Jam'iyyar PDP.

A daidai lokacin da rikicin shugabanci ke ci gaba da galabaita babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, wato PDP, wasu manya 'ya'yanta sun ce rikicin abu ne da aka saba da yi a jam'iyyar, kuma zai wuce ba da dadewa ba.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Nasir Ibrahim Mantu, , wanda yanzu ke cikin kwamitin da aka ba wa aikin gyaran kundin tsarin mulkin jam'iyyar, ya ce suna gab da kammala aikin da aka ba su, lamarin da ya ce zai taimaka wajen dawo da martabar jam'iyyar.

A hirarsu da Haruna Shehu Tangaza na BBC, Sanata Mantu ya ce a yanzu jam'iyyar na nadamar kura-kuran da ta tafka lokacin da take mulki, amma yanzu ta shiga taitayinta.

Kuma a shirye ta ke ta nuna 'yan Nigeria hakan a aikace matukar ta sa ke samun dama nan gaba.

Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti