Ana tababa kan sasanta rikicin Syria

Ban ki Moon Hakkin mallakar hoto un
Image caption Fararen hula na shan wahala a rikicin da ake yi a Syria.

Taron tattaunawa dan magance rikicin Syria da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya budewa yau Juma'a a Geneva ya gamu da turjiya.

Tawagar da ke wakiltar 'yan adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, sun yi barazanar kauracewa taron har sai gwamnatin Syria ta dakatar da ruwan bama-baman da take yi a yankunan fararen hula, tare da 'yanta mata da kananan yara da suka makale a garuruwan da aka yi wa kawanya.

Majalisar Dinkin Duniya na fatan tattaunawa da dukkan bangarorin biyu kafin karshen watan nan.

To sai dai kuma tuni Amurka ta fusata 'yan adawa, kan cewa kafa sharadi a tattaunawar da za a yi bai dace ba, amma za su iya sanya batun yarjejeniyar tsagaita wuta a bangaren sulhu domin kawo karshen wahalar da fararen hula ke ciki a kasar Syria.