A kawar da son zuciya — Ban ki Moon

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban KI Moon

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki moon, ya yaba da tattaunawar da ake yi a kan Syria a Geneva.

Mista Ban Ki Moon ya kara da cewa "mata da yara su suka fi shan wahala a yakin da ake yi, don haka lokaci ya yi da yakamata a kawo karshensa, da kuma dukkannin abubuwan keta mutuncin adam da ya kankane yakin".

Babban Sakatare Ban Ki Moon ya ci gaba da cewa, tuni ya kamata a yi wannan tattaunawar, sannan ya yi kira ga bangarorin biyu da ke fada da juna da su kawar da son zuciya, sannan su fifita bukatun mutanen Syria a kan na su.