Wasila ta haihu

Hakkin mallakar hoto Al Amin Ciroma
Image caption Wasila da Mijinta Al Amin Ciroma da kuma jarirya Ruqayya. Al Amin dan jarida ne kuma tsohon dan wasan kwaikwayo

Fitacciyar 'yar wasan kwaikwayon nan Wasila Isma'il ta haihu.

A hirar da BBC ta yi da mijinta Al Amin Ciroma ya ce, Wasila ta haifi mace a ranar Juma'a, har ya sa mata suna Ruqayya.

Al Amin ya kuma kara da cewa, uwar da jaririyar lafiyarsu kalau.

Kafin ta yi aure, tauraron Wasila ya haska sosai a lokacin da ta ke fitowa a fina-finan Hausa, jarumar ta yi farin jini a lokacin da ta fito a wani fim mai suna 'wasila' a shekarun 1990.