An tabbatar da rasuwar mutane 65 a Dalori

Image caption An kone galibin gidajen kauyen Dalori

Hukumar da ke kula da bayar da gajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce mutane sittin da biyar ne suka mutu sakamakon harin da aka kai a garin Dalori na jihar Borno.

Sanarwar da NEMA ta fitar wacce Sani Datti ya sanyawa hannu, ta ce akalla mutane 136 ne suka samu raunuka sakamakon hare-haren da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai.

Sai dai tun a ranar Lahadi, wani babban jami'in hukumar a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Muhammad Kanar ya ce 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin ranar Asabar da misalin karfe bakwai na dare.

Ya kara da cewa "Bayan an kai harin mun dauko gawarwakin mutane 36 yayin da 'yan kungiyar kato-da-gora, wato Civilian JTF suka dauko gawarwakin wasu mutane."

Muhammad Kanar ya ce duk wanda yake shakkar wadannan alkaluma, zai iya zuwa asibitin da aka ajiye gawarwakin domin ganinsu.

A cewarsa, mutanen da suka tsira daga harin sun koma cikin garin, kuma an kai musu kayayyakin abinci.

Ga hirar da muka yi da Mohammad Kanar

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti