Barayin namun daji sun harbe matukin jirgi

Image caption Taswirar inda hadarin ya faru; gandun namun daji na Maswa da ke kasar Tanzania. Ana zargin barayin na kashe giwaye ne domin haurensu.

Wasu masu satar namun daji a Tanzania, sun harbe wani matukin jirgin sama mai saukar ungulu.

Matukin jirgin Roger Gower, ya na aiki ne da wata kungiyar agaji mai kula da naman daji a kasar.

Kungiyar kula da namun dajin ta ce, masu satar namun dajin sun harbi jirgin mai saukar ungulu ne da Roger ya ke tukawa, a yayin da ya ke bin diddiginsu.

Abokin aikinsa ya ce masu satar namun dajin sun harbe shi ne a yayin da jirgin ke bi ta kan gawar wata giwa daga sama, wacce barayin suka kashe.

Mista Gower ya samu nasarar sakko da jirgin kasa, amma kafin a kai masa dauki ya mutu.

Wani dan majalisa kuma tsohon Ministan albarkatu na kasar, Lazaro Nyalandu ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya kara da cewa, hadarin ya faru ne a gandun namun daji na Maswa, mai iyaka da babban gandun namun daji na Serengeti da ke arewacin Tanzania.

Ofishin kula da harkokin waje na Biritaniya ya tabbatar da mutuwar matukin, ya kuma ce ya na kokarin taimakawa iyalan mamacin.