AU ta dakatar da tura soji zuwa Burundi

Babban Taron Kungiyar AU

Kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta dakatar da wani shiri na tura ma'aikatan kiyaye zaman lafiya dubu biyar a Burundi domin kwantar da tashin hankalin da aka kwashe watanni 9 ana yi wanda kuma a cikinsa aka kashe daruruwan mutane.

Shugabannin Afrika dake halartar wani taron koli a Addis Ababa na tattaunawa kan shrin da aka tsara a cikin watan Disamba, wanda ya bayar da shawarar tura sojin koda kuwa babu izinin gwamnatin da za ta karbi bakuncinsu.

Shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza ya ce zai dauki duk wani tsoma bakin kungiyar ta AU a matsayin wani yaki.

A wajen taron kolin, wani babban jami'in kungiyar ta AU, Ibrahima Fall, ya ce ba ta taba zama aniyar kungiyar ta AU ta tura masu aikin kiyaye zzaman lafiyar ba tare da yardar gwamnati ba.