Yunkurin kawar da bata-gari a jihar Lagos

Ofishin 'yansanda a Najeriya
Image caption Ofishin 'yansanda a Najeriya

Hukumomi a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya sun ce sun fara yunkurin dakile barazanar da gungun matasa bata-gari ke yi ga ga al'ummar jihar.

Hukumomin da hadin gwiwar wasu al'ummar jihar ne suka fara wannan yunkuri.

Wannan dai ya zo ne bayan bullowar wasu matasa da ake kira 'One Million Boys' da ke tafka ta'asa a jihar.

Matasan dai na yin gungu-gungu cikin dare suna rarraba kawunansu zuwa shiyyoyi da ke garin na Lagos suna yin fashi ko sata.

Rahotanni sun ce mafi muni daga cikin ayyukansu shi ne yadda idan sun shiga gidajen haya su kan matsawa ma'aurata yin lalata da matan auren da ba nasu ba.

Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta ce kawo yanzu ta gano maboyar wadannan miyagun mutanen kuma ta fara daukar matakai a kansu.