Takaitaccen tarihin Cheffou Amadou

An haramtawa Cheffou Amadou tsayawa takara a 1993

Asalin hoton, Niger

Bayanan hoto,

An haramtawa Cheffou Amadou tsayawa takara a 1993

An haifi Cheffou Amadou a 1942 a Kornaka na jihar Dakoro da ke yankin Maradi. Ya karanta ilimin tukin jiragen sama a Faransa.

Bayan babban taron kasa na Conference Nationale a 1991, mahalarta taron sun zabi Cheffou Amadou a matsayin Firayi ministan rikon kwariya daga 1991 zuwa 1993.

Bai yi takara ba a zaben shugaban kasa na farko a 1993 saboda taron na Conference nationale ya haramta ma shi tsayawa takara.

Kafin ya zama Firayim minista, Cheffou Amadou ya rike mukamin wakilin Kungiyar kula da zurga-zurgar jiragen sama ta duniya, a Yammaci da Tsakiyar Afrika.

Har zuwa shekara ta 2002, shi ne Direktan Kungiyar a Yammaci da Tsakiyar Afrika inda ya zauna a birnin Dakar na Senegal.

Ya kafa jam'iyyar RSD-Gaskiya a watan Janairun 2004, bayan ya fice daga jam'iyyar CDS-Rahama inda yake rike mukamin mataimakin shugaban jam'iyya na kasa.

A zaben shugaban kasa na 2004, ya zo na hudu daga cikin 'yan takara shidda, amma ya ci zaben 'yan majalisar dokoki na shekarar.

Bayan shugaba Mamadou Tandja ya kafa majalisar kansiloli masu bada shawara ga gwamnati, CESOC a 2006, ya nada Cheffou Amadou a matsayin shugaban Majalisar har zuwa 2010.

Ya tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2011, kuma a zagaye na biyu ya goyi bayan Mahamadou Issoufou, dan takarar jam'iyyar PNDS-Tarayya.

A ranar 24 ga watan Agusta na 2011, an nada Cheffou Amadou a matsayin Mai shiga tsakani na kasa.

A ranar 13 ga watan Disamba na 2015 ne, jam'iyyar RSD-Gaskiya ta tsaida Cheffou Amadou a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben ranar 21 ga watan Fabrairu na 2016.