EFCC ta kai samame ofishin Namadi Sambo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sambo tare da tsohon shugaba Jonathan

Jami'an hukumar yaki da rashawa a Najeriya, EFCC, sun kai samame ofishin tsohon mataimakin shugaban kasar Muhammadu Namadi Sambo, a Abuja.

Wata majiya mai karfi ta tabbatarwa BBC cewa jami'an EFCC din sun kai samamen ne a wani ofishin Sambo na kashin kansa a Abuja, a ranar Asabar din da ta wuce.

Bayanai sun ce EFCC ta kai samamen ne a ci gaba da binciken da take yi kan batun karkatar da kudaden sayo makamai da ake zargin wasu jami'an tsohuwar gwamnatin Jonathan.

Sai dai wata majiya ta ce jami'an EFCC sun dauki wasu takardun da suka shafi kwangiloli a lokacin da Namadi Sambo yake gwamnan jihar Kaduna.

A yanzu haka dai wasu manyan kusoshin tsohuwar gwamnatin Jonathan na fuskantar shari'a a gaban kotu, bisa zargin almundahana da sama da dala biliyan biyu wadanda aka ware domin sayen makamai na yaki da 'yan Boko Haram.