Buhari ya mayar da martani kan harin Dalori

Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta ce harin da mayakan Boko Haram suka kai a kauyen Dalori da ke kusa da birnin Maiduguri wanda ya hallaka mutane masu dimbin yawa, ba zai kawar da maganar da shugaban kasar ya yi cewa sojojin kasar sun karya-lagon kungiyar ba.

Kakakin fadar shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kai wannan harin ne a kokarin da suke yi na shigowa garuruwa domin su buya saboda irin yadda sojoji ke fatattakarsu daga dajin Sambisa.

Malam Garba Shehu ya ce wannan lamari da ya faru ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ciwo, sannan ya aika da sakon ta'aziyya da jaje ga iyalan mutanen da wannan hare-hare ya rutsa da su.

Kakakin fadar shugaban kasar ya ce ya kamata mutane su kasance masu sanya ido a kan duk wani mutum da suka ga ba su yarda da shi ba, sannan a rinka kula a dukkan wajen da ake taruwar jama'a na irin mutanen da ke wajen domin gujewa sake faruwar wannan lamari.

Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an sojin Nigeria ke ikirarin kary- lagon 'yan Boko Haram din a yankin arewa maso gabashin kasar.