Bakaken beraye na yaduwa saboda sare gandun daji

Hakkin mallakar hoto Life on white Alamy
Image caption Bakaken Beraye na yaduwa saboda sare gandun dazuka

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa sare gandun dazuka na kara haifar da yaduwar bakaken beraye.

Binciken - wanda aka yi a yankin tsibirin Borneo - ya nuna cewa sare itatuwan na janyo berayen ne saboda bishiyoyin da suka fadi na kunshe da kwarin da berayen kan yi kalaci da su.

Kazalika yin hakan na samar da maboya ga berayen da ma dangoginsu.

Masu binciken kimiyya sun ce karuwar berayen na yin barazana ga sauran dabbobi da kuma tsuntsayen da ke kwanci.