Kasar da ke kyautar ido ga kasashen duniya

Image caption Wasu daga cikin malaman buda na kira ga 'yan kasar su ba da gudunmawar wasu gabobin jikinsu bayan mutuwa

Idan ido ya samu matsala, likitocin da zasu gyara shi na bukatar a dasa wani bangare na ido kamar kwayar ido da abin da ya rufe ta daga wani wanda ya mutu.

Akwai karancin masu bayar da ido a duniya, saidai kasa daya wato Sri Lanka ta yi zarra wajen hakan ba tare da ko sisi ba.

An rufe idon Paramon Malingam na dama da bandeji, yayin da kwalla ke fita daga dayan idon, wannan kukan farin ciki ne ga mutumin da ya yi gamo da katar.

Ya ce "Na yi tsammani zan kare sauran rayuwa ta da ido daya ne."

Paramin wani mai shago ne a tsakiyar Sri Lanka, kuma ya fadi hakan ne domin shekaru goma sha uku da suka wuce ya samu rauni a ido.

Haka kuma a bara ma ya sake samun rauni a wannan idon, amma samun kyautar fatar da ke rufe kwayar ido wato cornea a turance ya cece shi?

Fatar ta cornea na da muhimmanci wajen gani, kuma idan ta samu matsala to babu abin yi sa dai ayi dashenta.

Sai dai samun wanda zai baka kyauta abu ne mai wuya a duniya, musamman saboda ba fatar bata dadewa ta ke lalacewa.

A don haka dole a cire idon mamaci sa'oi kadan bayan mutuwarsa, haka kuma dole a dasa wa mutum cornea cikin makonni hudu da ciro shi, kuma hakan ma ya danganta da yadda aka adana fatar.

A babban asibitin ido na Sri Lanka inda Paramon ke jinya, kuma can a sashen adana ido wata daliba Viswani Pasadi na cike wata takarda domin bayar da kautar idonta bayan ta mutu.

Viswani na bin addinin Buda kamar mafi yawan 'yan kabilar Sinhalese wadanda su ne kashi 75 na al'ummar Sri Lanka.

Kuma ta yi imani cewa ana sake haihuwar mutum bayan ya mutu, ta ce "Idan na ba da ido na a wannan rayuwar, to zan fi gani sosai a rayuwa ta gaba."

Wani likita Hudson Silva mai aiki tare da wata kungiya mai zaman kanta da ke karbar kyautar ido a Sri Lanka ya bayyana cewa, ko wane mutum daya cikin biyar a Sri Lanka ya yi alkawarin bayar da idonsa.

Kuma hakan bai hada da irinsu Viswani ba da suka bayar da kyautar ga hukumomin gwamnati ko wasu kungiyoyin na daban.

Zakuwar da mutanen Sri Lanka suka yi na bayar da kyautar idonsu yasa da dadewa kasar ta tara fiye da idanun da take bukata, inda har take kai wa kasashen waje.

Haramun ne a cire wani bangare na jikin mamaci a kasashen Musulmi, saboda haka kasashen Pakistan da Masar su ne suka fi kowacce kasa karbar kyautar ido daga Sri Lanka.

Yayin da Malaysia da Najeriya da Sudan ke cikin jerin kasashe hamsin da ke karbar kyautar ido daga kasar ta Sri Lanka.