Cameron ya yi tsokaci kan matsayinsu a EU

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Cameron ya yi murna kan daftarin da aka gabatar

Firai ministan Biritaniya David Cameron ya ce kasarsa za ta iya yi zaben raba gardama kan zamowarta cikin tarayyar turai a cikin 'yan watanni masu zuwa.

Firai ministan ya fadi hakan ne bayan da aka gabatar da daftarin wasu shawarwari wadanda manufarsu ita ce shawo kan Biritaniya ta ci gaba da zama cikin kungiyar tarayyar Turan.

Mista Cameron ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan daftari.

"Kan batutuwa da dama an sha gaya min cewa wadannan bukatu ba masu yiwuwa ba ne. Mutane suna ganin kamar ba za mu samu abin da mu ke so ba. Amma wannan daftari ya nuna cewa akwai alamun nasara," in ji Cameron.

Mr Cameron ya yaba da abin da aka gabatarwa Biritaniya, amma kuma Nigel Farage, shugaban jam'iyyar adawa ta UKIP ya bayyana batun a matsayin abin takaici.

Shawarwarin sun hada da wani tsari wanda zai bai wa Biritaniya damar dakatar da biyan wasu kudaden walwala ga ma'aikata 'yan ci-rani.

Sai dai kafin su fara aiki, wajibi ne sai daukacin kasashen tarayyar 28 sun mara baya ga sauye-sauyen yayin wani babban taro da za a yi nan da makonni biyu.