Karancin abinci da magani a Fallujah

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yaki ya daidai ta Fallujah

Jami'ai da kuma mazauna garin Fallujah da ke yammacin Iraki sun ce dubun-dubatar mutane a garin na fama da karancin abinci da man fetur da kuma magunguna.

Birnin dai yana karkashin ikon mayakan IS ne tun shekaru biyu da suka gabata, kuma tun a shekarar da ta gabata ne dakarun gwamnati da mayakan sa-kai na Shi'a suka yi wa garin kawanya da taimakon hare-haren sama na gamayyar kawancen da Amurka ke jagoranta.

Gwamnan yankin Anbar Sohaib al-Rawi, ya yi kira ga gamayyar kawancen da su dinga jeho kayan agaji daga sama.

Wani jami'in jin kai na majalisar dinkin duniya a Iraki ya bayyana lamarin da cewa ya yi matukar tsanani.