Jirgin sama ya yi saukar gaggawa a Somalia

Jirgin saman fasinja a Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jirgin saman fasinja a Somalia

An tilastawa wani jirgin saman fasinja saukar gaggawa a kasar Somalia, bayan da wata fashewa da ta haddasa bula a tsakiyar jirgin.

An ambato Matukin jirgin dan kasar Serbia Vladimir Vodopivec,na cewa yana jin bam ne ya haddasa fashewa.

Mutane biyu ne aka bada rahoton cewa sun jikkata a lamarin da ya faru jim kadan bayan tashin jirgin daga Mogadishu babban binin kasar ta Somalia.

An kuma samu nasarar kubutar da sauran fasinjojin 74.

Wadanda ke cikin jirgin sun bayyana yadda suja ji wani babban kara, inda bakin hayaki ya biyo baya.