Abubuwa biyar da ya kamata ka sani a kan Ted Cruz

Hakkin mallakar hoto Getty

An yi ta magana kan nasarar da Donald Trump na jam'iyyar Republican ya samu a kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da zaben shugaban kasar Amurka, amma sai ga shi Ted Cruz ya doke shi a jihar Iowa. To ko wanene Ted Cruz?

An haifi Ted a Canada

An haifi Rafael Edward Cruz a Calgary da ke Canada, sai dai ya samu shiga takarar shugaban kasar Amurka ne domin mahaifiyarsa Ba Amurkiya ce.

Wato yana da shaidar zama dan kasa na kasashen biyu.

Mahaifinsa dan gudun hijirar kasar Cuba ne wanda ya tsere wa gwamnatin Batista.

Kuma sun zauna ne a Houston da ke jihar Texas a shekarar 1974, lokacin Rafael na da shekaru 13.

Tun daga wancan lokacin ne ya gajarta sunansa na biyu zuwa Ted.

Ya yi gagarumin aiki a mukaminsa na farko

Cruz ya yi karatu a jami'ar Princeton, kuma ya yi aikin lauya har ta kai shi ga rike mukamin atoni na wata gunduma a shekarar 2012.

Haka kuma ya zamo sanata yana da shekaru 42.

Duk da cewa ya yi dauki kasa da shekaru hudu yana aiki, ya yi farin jini sosai ta yadda mutane da dama suka zo suna kaunar yadda yake siyasarsa.

Haka kuma ya samu wadanda ba sa ga maciji da juna, ciki har da 'yan jam'iyyarsa.

Duk da cewa wannan ne wa'adin Ted na farko a matsayin sanata, amma kuma ya taka rawa wajen "Yadda ayyukan gwamnatin tarayya suka tsaya cik a shekara ta 2013"

Ya shiga cikin zazzafar mahawara kan batun shirin gwamnatin Amurka kan jirage marasa matuka, inda Sanata John McCain ya yi masa lakabi da "wacko bird."

Sannan ya yi jawabi na tsawon sa'oi 21 a zauren majalisa, a wani yunkuri na jinkirta ko rage kudaden da za a kashe a shirin samar da lafiya na kasar.

Ya yi kira ga jam'iyyar Tea party

Hakkin mallakar hoto Getty

Mista Cruz ya sanar da aniyarsa ta shiga takara a jami'ar Christian Liberty, inda ya yi alkawarin ba zai sauya manufofinsa ba don a zabe shi.

Kuma hakan ya aike da sako ga jam'iyyun Christian social party da tea party, abin da ya taimaka masa samun nasara a zaben da aka yi.

Muhimman abubuwan da Mista Cruz ya ce zai yi idan har ya zama shugaban kasa sun hada da maida kudin haraji kashi goma cikin dari ga kowa da ruguza yarjejeniyar da aka cimma da Iran kan makaman Nukiliya, kana kuma zai janye garambawul din da Obama ya yi wa tsarin kiwon lafiya na kasa.

Ted mutum ne mai matukar goyon bayan yin garonbawul ga dokar mallakar bindiga.

Kuma zai mayar da mutane da dama kasashensu, tare da kare bakin iyakar Amurka da Mexico.

Goyon bayan gamayyar jam'iyyu

Idan da ace Mista Cruz bai samu nasara ba a Iowa to da hakan ya kawo nakasu ga kamfe din da ya ke yi.

Amma nasarar da ya samu na nuna cewa akwai hadin kai tsakanin magoya bayan jam'iyyun evangelica da tea party da liberty.

Kuma hakan zai kara fitowa bayan fafatawar da za a yi nan gaba a wasu jihohin, inda za su fito da wanda suke so.

Mista Cruz na da kudaden yakin neman zabe da suka kai $20 miliyan, yayin da yake taimaka wa wasu kwamitocin da wasu kudaden da suka fi haka.

Ya gina tsarin yakin neman zabensa na tsawon jadawalin zaben fitar da gwani da kuma yadda idan ta kama zai yi hammaya gaba-gaba da Mr Trump da kuma Mr Rubio mutumin da ke samun goyon bayan manyan 'yan kasuwa da attajiran kasar.

Zai iya doke Donald Trump

Hakkin mallakar hoto Getty

Hakan dai a bayyane ya ke tun da gashi har ya samu nasara a Iowa, sai dai rashin nasarar Trump a farkon yakin neman zabe abu ne mai muhimmanci.

Da fari mista Trump yana samun nasara a Iowa a lokacin da aka yi kuri'ar jin ra'ayin jama'a, amma daga karshe yawan sabbin mutanen ya yi tsammanin za su kada masa kuri'a basu kai hakan ba.

Wadanda suka jima a cikin jam'iyyar Republican suna nuna damuwa kan irin gwamnatin da Trump zai kafa saboda ba a san alkiblar siyasarsa ba.

A waje daya kuma suna nuna damuwa kan irin gwamnatin da Cruz zai kafa, saboda sun san mutum ne da zai fifita akidojinsa a kan na jam'iyyya.

Domin zai zama shugaban kasa mai ra'ayin rikau da aka taba zaba a wannan zamani.