Cruz ya bai wa Trump mamaki a Iowa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gabanin zaben, an yi tsammani Mista Trump ne zai lashe shi.

Sanatan jihar Texas ta Amurka, Ted Cruz, ya samu kuri'u mafi rinjaye a fafatawar zaben fitar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Republican a jihar Iowa.

Mista Cruz ya samu kashi 28 bisa dari na kuri'un 'yan jam'iyar ta Republican, inda ya yi galaba kan abokin karawarsa Donald Trump, wanda ya samu kashi 24 bisa dari.

Marco Rubio na jihar Florida- ya zo na uku da kashi 23 bisa dari na kuri'un da aka kada, fiye da yadda a baya aka yi hasashen zai samu.

Gabanin zaben dai, an yi tsammanin Mista Trump ne zai lashe shi.

Sai dai MistaTrump din ya ce yana da yakinin zai samu galaba daga karshe.