Cutar Zika ta bulla a Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jariri mai dauke da cutar Zika

Mahukunta a jihar Texas ta Amurka sun ce a karon farko kwayar cutar Zika, wacce sauro ke yadawa, ta bulla a jihar.

Sun ce akwai yiwuwar an samu yaduwar kwayar cutar ne ta hanyar jima'i, saboda wanda ya kamu da ita bai yi tafiya zuwa kasar waje ba, amma kuma ya yi mu'amala da mai dauke da cutar a lokacin yana wajen kasar ta Amurka.

Sun kara da cewa akwai bukatar kara kaimi wajen wayar da kan jama'a a kan cewar ana iya yada cutar ta Zika ta hanyar jima'i.

Sauro ne dai aka sani da yada kwayar cutar, wacce ake dangatawa da annobar haihuwar yara masu tawaya a kasar Brazil.

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO ta ce annobar ta zama wacce ke neman daukin gaggawa ta duniya.