Mutane biliyan daya ne ke amfani da WhatsApp duk wata

Image caption Masana sun ce har yanzu WhatsApp na fuskantar kalubale.

Kamfanin Facebook ya ce mutane biliyan daya ne ke yin amfani da manhajar WhatsApp, wadda mallakin Facebook ce, a duk wata.

Sun bayyana cewa manhajar ta fi takwararta ta Facebook Messenger, wacce mutane miliyan 800 ke amfani da ita a duk wata.

Kamfanin ya ce ana aikawa da sakonnin tes biliyan 42, yayin da ake aikawa da sakonnin bidiyo miliyan 250 a manhajar ta WhatsApp a kowacce rana.

Sai dai masu sharhi sun ce har yanzu WhatsApp na bayan wasu manhajojin.

Wani mai sharhi kan amfani da wayoyin salula, Jack Kent, ya ce, "Akwai wurare da dama da mahnajar WhatsApp ba ta yin tasiri. Manhajar WeChat da ke China tana da masu amfani da ita sama da miliyan 500 million, yayin da kuma manhajar Line ta samu karbuwa a Japan, haka kuma manhajar Kakao Talk ke tasiri sosai a Koriya ta Kudu. Amma duk da haka manhajar WhatsApp ta fi karbuwa a duk duniya."