'Isra'ila na tura 'yan ci-rani zuwa Afrika'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sansanin 'yan ci-rani na Holot a Isra'ila

Sashen BBC na Afrika ya samu shaidu da suka nuna cewa kasar Israi'la na turo wasu 'yan Afrika da ke ci-rani wadanda ba a maraba da su, zuwa wata kasa ta daban a wani shiri da ake yi a asirce, wanda kuma mai yiwuwa ya saba wa dokokin kasa da kasa.

A yanzu haka akwai kimanin 'yan ci-rani dubu 45 'yan kasar Eritrea da Sudan da ke kasar Isra'ila.

Gwamnatin Isra'ila ta ki ta bayyana ko wacce kasa ce aka shirya wannan tsarin da ita.

Sai dai BBC ta tattauna da wasu mutane wadanda suka ce an tura su zuwa Rwanda da kuma Uganda.

A cikin tsarin, Isra'ila tana bai wa mutanen dala dubu uku da rabi kafin a tisa keyarsu zuwa filin jirgin saman Tel Aviv.