Jirgin helikofta ya yi hatsari a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Helikoftan da ya yi hatsari bara a Lagos

Hukumar kula da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta tabbatar da cewa wani jirgi mai saukar angulu (helikofta) ya yi hatsari a kan hanyarsa ta zuwa birnin Lagos daga birnin Fatakwal.

Kakakin hukumar ta NEMA a Lagos, Ibrahim Farinloye ya ce mutane 11 ke cikin jirgin, to amma an samu nasarar kubutar da su duka.

Bayanai sun ce jirgin mai saukar angulu mallakar kamfanin Bristow Helicopter ne.

Shi ma kakakin hukumar bincike kan hadduran jiragen sama AIB, Tunji Oketunbi ya ce tuni suka soma binciken abin da ya janyo jirgin ya fadi.

A shekarar da ta wuce ma, wani helikofta din mallakar kamfanin Bristow Helicopter ya fadi a cikin ruwa a Lagos, lamarin da ya janyo mutuwar mutane shida daga cikin su 12 da ke cikin jirgin.