Dubban 'yan gudun hijirar Syria sun tafi Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kananan yara na cikin wadanda rikicin Syria ya fi shafa.

Mahukunta a Turkiyya sun ce dubban 'yan gudun hijirar Syria sun nufi kan iyakar Turkiyya a yunkurin da suke yi na kaucewa yakin da ake yi a birnin Aleppo.

A 'yan kwanakin da suka wuce dai, jiragen yakin Rasha sun taimakawa sojin Siriya suka kara nausawa zuwa yankin na Aleppo.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka a kan ci gaba da kai hari da Rasha ke yi a kasar ta Syria, yana cewa hakan ya sanya duk wani yunkurin zaman lafiya ya zama bai da wani amfani.

'Za a taimaka wa Syria da biliyoyin dala'

A ranar Alhamis ne ake gudanar da wani babban taro a birnin London inda za a tara dala biliyan tara domin taimakawa 'yan gudun hijirar Syria.

Ana yin taron ne kwana guda bayan an tashi baram-baram daga wajen wani taro kan yadda za a dakatar da yakin basasar kasar, wanda majalisar dinkin duniya ta dauki nauyin gudanar wa.

Kasar Biritaniya ta bayyana cewa za ta bayar da gudunmawar dala biliyan daya da miliyan dari bakwai ga miliyoyin mutanen da rikicin Syria da na makwabtan kasar ya shafa.

Firayim Ministan Biritaniya, David Cameron, ya ce kashe kudin kan mutanen zai sa su daina yunkurin barin kasar zuwa wasu kasashen Turai.

Ministan harkokin wajen Norway, Borge Brende, ya yi gargadin cewa dole a samu nasara a taron na yau, idan ba haka ba za a fusakanci kalubale mai yawa.