CAR: Sojoji sun ci zarafin yara

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana zargin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da cin zarafin yara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gano wasu sabbin laifukan cin zarafi har guda bakwai da dakarun wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Tsakiyar Afurka suka aikata ga kananan yara.

Lamarin ya faru ne a birnin Bambari, inda biyar daga cikin bakwai din suka shafi kananan yara, ya yin da hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce gungun dakarun wanzar da zaman lafiyar sun yi wa wasu daga cikin yaran Fyade.

Dan haka Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta komar da yawancin dakarun ta gida daga jamhuriyar tsakiyar Afurkan.

Fiye dakarun wanzar da zaman lafiya 100 ne aka rawaito majalisar Dinkin Duniya ta ambato za su koma gida, saboda samunsu da laifin ta'asa a Jamhuriyar Tsakiyar Afurka maimakon gabatar da ainahin aikin da aka kai su yi.

Majalisar Dinkin Duniya tace bayan gudanar da wannan bincike na cin zarafin yara, akwai kuma wani binciken na daban na aikata fyade har sau takwas, kuma ko a kwanakin baya an gudanar da bincike kusan guda 21 duk dai kan batu guda.