Clinton da Sanders sun yi muhawara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanders ya ce Mrs Cliton 'yar takarar "manyan kasa" ce, sai dai ita kuma ta ce ba zai iya mulkin Amurka ba.

Mutane biyu da ke son yin takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton da Bernie Sanders, sun bayyana ra'ayoyin da suka sha bam-ban da na juna a game da tattalin arziki da manufofin harkokin kasashen waje.

Mutanen biyu sun yi hakan ne a muhawararsu a talabijin ta farko ta gaba-da-gaba a jihar New Hampshire tun bayan da suka zamo su biyu ne kawai ka iya yi wa jam'iyyar takara.

Mrs Clinton ta ce Sanders mutum ne mai tunani mai kyau amma ba zai iya yin mulkin kasar ba, sai dai Mista Sanders ya bayyana Mrs Clinton a matsayin 'yar takarar da "manyan kasar suka tsayar" domin ta biya bukatunsu.

Mrs Clinton ta ce shirye-shiryen Bernie Sanders, musamman na samar da inshorar lafiya ga kowa da kowa suna da matukar tsada, kuma ba masu yiwuwa ba ne.

Mista Sanders, dan majalisar dattawa daga jihar Vermont, ya soki Mrs Cliton kan abin da ya kira mara baya ga yakin da aka yi a Iraki, sai dai ita kuma tana nuna tantama kan kwarewarsa game da manufofinsa na kasashen waje.

Mutanen biyu sun yi muhawar ne kwana biyar kafin a yi zaben da wakilan ke yi na jiha-jiha a karo na biyu, wanda za a yi a jihar ta New Hampshire.