'Gawa ta fado daga jirgin sama a Somaliya'

Hakkin mallakar hoto Harun Maruf
Image caption Hujin da aka samu a jirgin saman

'Yan sanda a Somaliya sun gano wata gawa a kusa da Mogadishu babban birnin kasar, da ake zato ta fado ne daga jirgin sama a ranar Talata.

Jirgin saman kamfanin Daalo ya yi saukar gaggawa, bayan wata fashewa da aka samu lamarin da ya janyo jirgin ya huje.

Mazauna garin sun ce sun gano gawar wacce ta fado kasa, abin da ya sa 'yan sanda suka soma bincike.

Sai dai har yanzu ba a san abin da ya jawo jirgin saman ya huje ba, jim kadan bayan da ya tashi.

Wani matukin jirgin na tunanin cewa watakila bam ne ya fasa shi.