Neman bindigar Zinare ta Gaddafi

A lokacin da 'yan tawayen Libya ke murnar mutuwar Muammar Gaddafi, an dinga nuna karamar bindigarsa ta zinare a matsayin wata alama ta samun nasara.

Inda 'yan tawayen suka dinga karba suna kallo.

Shekaru hudu bayan nan wakilin BBC Gabriel GateHouse ya sake komawa Libya, domin sanin ko wane hali mutumin da ya tsinci bindigar ke ciki.

Bindigar ta Gaddafi ta kasance a wancan lokaci tamkar wata alamar sauyin iko a wata sabuwar Libya.

Sai dai kasar a yanzu tana cikin rudani, domin an samu gwamnatoci masu gaba, kowa na kokarin ya karbe iko a kasar.

An kuma samu rarrabuwar kawuna a tsakanin masu banbancin akida da yankunan kasar da kuma masu son bin tsarin musulunci da masu son a raba mulki da addini.

Halin da ake ciki a Libya ne ya kai ga kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci ta IS, ta yi amfani da rashin gwamnatin ta karbe iko da mahaifar Gaddafi wato Sirte.

Ana cikin wannan hayaniyar ce Gabriel ya koma Misrata wanda ke da nisan kilomita 200 daga Tripoli, kuma birnin da ke da kwarya-kwaryar cin gashin kai.

Ya je birnin ne domin neman mutumin da bindigar zinaren ke hannunsa.

Da farko Gabriel ya fara ziyarar wani kusa a Misrata a lokacin juyin-juya- halin, kuma mutumin da aka kai wa gawar Gaddafi bayan dakarun 'yan tawayen sun kashe shi.

Shi kuma ya sanya gawar a cikin wani firgin ajiyar nama, inda mutane suka dinga zuwa suna kallonsa.

Muna kallon hotuna tare da Anwar sai ya kada baki ya ce "Yanayin da ake ciki sam babu kyau. "

Inda ya kara da cewa "Ana kukan targade ga karaya ta zo, domin an kashe Gaddafi amma matsalolin da suka biyo baya sun zarta na baya. Domin har yanzu muna neman abu guda ne wato samun shugaba adali. Sai dai kowa na son mulki, ga bindigogi ko'ina. Kai abin ba kyau!"

Na shaida wa Anwar cewa ina neman wanda bindigar Gaddafi ke hannunsa.

Sai ya shaida mini abin da ya faru da Omran Shabaan, daya daga cikin mayakan da suka kama Gaddafi, wanda a wasu hotunan da aka dauka a wancan ranar, an ji muryarsa yana kokarin hana a kashe marigayin.

Omran ya zamo tamkar wani gwarzo. An dauki hotonsa rike da bindigar, amma 'yan watanni bayana mutuwar Gaddafi, magoya bayansa sun kama Omran a garin Bani Walid, inda suka lakada masa duka tare da azaftar da shi.

Hakkin mallakar hoto

Sai dai raunukan da ya ji ne suka yi sanadiyyar mutuwarsa a wani asibiti da ke Faransa, bayan an sake shi.

Daga karshe dai na sadu da mutumin da na ke nema Mohammed Elbibi, wanda ya dauko bindigar ya kuma nuna mini. Mohammed ya yi amanna cewa daya daga cikin 'ya'yan Gaddafi ne ya ba tsohon shugaban kasar domin taya shi murnar bikin cikarsa shekaru 32 da juyin mulki.

Sai dai shekaru goma bayan Marigayi gaddafi ya samu kyautar bindigar, Mohammed Elbibi ya yi ta nuna wannan bindigar a matsayin wata alama da ta kawo karshen mulkin Marigayi Mu'ammar Gaddafi a Libya.