An kama dillalan miyagun kwayoyi a Kaduna

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, NDLEA shiyyar Kaduna ta ce ta kama wasu masu sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi su 25 a jihar.

Hukumar ta nuna wa manema labarai wasu tarin kwayoyi ciki har da hodar iblis, watau Cocaine da kuma tabar wiwi da ta ce ta kwace su ne daga hannun dillalan kwayoyi a jihar.

Gwamnatin jihar Kaduna dai na cewa a kokarin magance tafka manyan laifuffuka ne ta hada gwiwa da hukumar NDLEA, abin da ya haifar da wannan kame.

A watan da ya wuce ma, a jihar Kano da ke makwabtaka da Kaduna, rundunar 'yan sanda a jihar ta ce ta kwato miyagun kwayoyi da suka kai Naira biliyan daya da miliyan dari 200 a cikin watanni biyu da suka wuce.

Rundunar ta ce ta kuma yi nasarar kama dillalan kwayoyi, ciki har da masu sayar da hodar ibilis.

Ga rahoton Nurah Mohammed Ringim daga Kaduna.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti