MTN na neman sasantawa da NCC

Image caption An ci tarar MTN ne saboda ya ki yanke layukan mutanen da ba su yi rijista ba.

Tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari'a na Amurka Eric Holder shi ne yanzu ke jagorantar sasanta wa tsakanin hukumomin Nigeria da kamfanin sadarwa na MTN.

Eric Holder ya shiga cikin lamarin ne a kokarin da kamfanin ke yi na neman a yafe masa ko kuma a rage tarar dala Biliyan uku da Miliyan dari tara da hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC ta sanya wa kamfanin.

Shi dai Mista Eric Holder ya kasance daya daga cikin mukarraban gwamnatin shugaba Barack Obama tun daga shekarar 2009 zuwa 2015, inda kuma yanzu ya koma ci gaba da aiki a matsayin lauya mai zaman kansa da ya shahara a harkar da ta shafi hukumomin sa ido na duniya.

An ci MTN tarar ne sakamakon kin yanke layukan wayar mutanen da ba su yi rijista ba har wa'adin yin rinjistar ya wuce.

Masana dai na ganin wannan tara ita ce mafi girma da aka taba sanya wa wani kamfanin sadarwa a Nigeria.

Layin MTN shi ne mafi shahara cikin layukan wayar sadarwa da aka fi amfani da shi a Nigeria, kuma rashin cimma wa'adin da hukumar NCC ta ba da kan yi wa mutane rijistar layin su ko kullewa shi ya janyo wannan takaddama tsalanin MTN da NCC.