Ba zamu sake zuwa kotun ICC ba - Ouattara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tuhumar abokin hamayyar Shugaba Ouattara, Laurent Gbagbo a kotun ICC

Shugaban Kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya ce ba zai sake tura wasu karin 'yan kasar zuwa Kotun manyan Laifuka ta Duniya ICC dake Hague ba

Ya yinda yake magana a Paris a lokacin da yake ganawa tare da takwaransa Francois Hollande, Mr Ouattara ya ce a yanzu Ivory Coast tana da abinda ya bayyana da tsarin shari'ar ta da yake aiki.

Ya kara da cewa cewa za'a gudanar da duk wasu shari'oi na gaba ne a kotunan kasar a cikin kasarsa

Abokin hamayyar Mr Ouattara, Laurent Gbagbo a yanzu na fuskantar zarge zargen aikata manyan laifuka akan bil-adama a kotun ta ICC. Sai dai Mr Gbagbo din ya musanta zarge zargen.

Mutane fiye da dubu 3 aka kashe a watanni biyar dinda aka shafe ana tashin hankali bayan zaben Shugabankasar 2010, a lokacin da Mr Gbbagbo ya ki amincewa da cewa ya sha kayi