'Rwanda na horas da 'yan tawayen Burundi'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana ci gaba da zaman dardar a Burundi

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya da aka kwarmata ya ce 'yan tawayen Burundi sun yi ikirarin cewa suna samun horo ne a Rwanda.

Rahoton wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu, ya ce an yi hira da wasu 'yan tawaye 18 wadanda aka dauka a wani sansanin 'yan gudun hijira a Rwanda, kuma a basu cikakken horo a kan sarrafa makamai.

'Yan tawayen sun ce burinsu shi ne su hambarar da shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza.

'Yan tawayen na Burundi sun fadawa kwararru na MDD cewa su kimani 400 ne aka ba su horo a Rwanda.

Rwanda ta yi watsi da zargin ta na mai cewa ba shi da tushe.