Nigeria: Shugaba Buhari ya tafi hutu

Image caption Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ne zai yi ayyukan shugaban a lokacin hutu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soma gajeren hutu daga ranar Juma'a 5 zuwa 10 ga wannan watan.

Sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar, ta ce a lokacin hutun, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai gudanar da ayyukan shugaban kasa.

Sanarwar ta ce tuni shugaba Buhari ya mika wasika ga shugaban majalisar dattawa da kuma ta wakilai domin sanar da su batun hutun, kamar yadda sashe na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.