Girgizar kasa ta daidaita kudancin Taiwan

Girgizar kasa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu.

Wa ta girgizar kasa ta daidaita birinin Tainan da ke kudancin kasar Taiwan, inda wani dogon gini mai hawa goma sha bakwai ya ruguzo tare da hallaka akalla mutane biyar.

Cikin wadanda suka rasu har da wani jariri dan watanni goma da haihuwa, jami'an kashe gobara sun yi nasarar ceton sama da mutane dari biyu daga ginin da ya ruguzo.

Sai dai har yanzu akwai mutanen da suka makale a cikin ginin, inda ma'aikatan ceto ke ci gaba da kokarin kubutar da su.

Girgizar kasar ta afkawa birnin Tainan ne da tsakar dare, a lokacin da yawanci mutane ke bacci.

Rahotanni sun bayyana cewa yawancin gine-ginen birnin sun ruguje.

Masu binciken yanayi na Amurka sun ce girgizar kasar na tafiya ne a hankali, wanda hakan ka iya kara yawan barnar da za ta yi.