'Yan Syria sun taru a iyakar Turkiyya

'Yan gudun hijirar Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kusan shekara biyar kenan ana yaki a Syria.

Dubban 'yan Syria da suka gujewa luguden wuta ta sama da gwamnatin kasar ke yi a kusa da birnin Aleppo, sun shafe daren farko a iyakar kasar da Turkiyya.

Turkiyya ta ce 'yan gudun hijira dubu goma sha biyar ne suka taru a Bab al-Salam, ya yin da wasu dubban ke ci gaba da fitowa daga Syria.

Wakilin BBC a kasar Turkiyya yace gwamnatin kasar ta yi amfani da sake kwararoruwar 'yan gudun hijira wajen dora laifin akan Rasha, wadda hare-hare ta sama da ta ke kaiwa a birnin Aleppo ya tilastawa mutane barin birnin.

A bangare guda kuma Turkiyya ta ki barin 'yan gudun hijirar su shiga kasar ta, amma ma'aikatan agajin kasar sun tsallaka iyakar Syria domin taimaka mu su da ruwa da abinci da kafa matsugunan wucin gadi.