Twitter ya rufe shafuka 125,000

Twitter Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyoyin 'yan ta'adda sun dade su na amfani da shafukan sada zumunta, wajen yada ayyukan su.

Shafin sada zumunta na Twitter, ya sanar da cewa ya rufe fiye da shafukan Twitter 125,000 da suke yada ayyukan ta'addanci tun a tsakiyar shekarar da ta wuce.

Kamfanin yace yawancin shafukan su na da alaka da kungiyar masu ikirarin kafa daular musulunci na IS.

Twitter ya yi ikirarin cewa saboda yada irin wadannan dabi'u shafin na su ke samun farin jini dan haka aka rufe su baki daya.

Kungiyoyin 'yan ta'adda sun dade su na amfani da shafukan sada zumunta aikawa da sakonnin su.

Haka kuma yawancin matasa da ke yin tattaki daga kasashen duniya dan shiga kungiyoyin 'yan ta'adda su na samun bayanan kungiyoyin ne a shafukan sada zumunta.