An sanya dokar ta-baci a Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Zimbabwe za ta shigo da masara daga Zambia.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya ayyana dokar ta-baci a yankunan karkarar da ke fama da matsalar fari.

Kasar dai tana fama da matsalar rashin ruwan sama tun shekarar da ta gabata, inda kiyasi ya nuna cewa mutane miliyan biyu da dubi dari biyar na matukar bukatar taimakon abinci.

Mista Mugabe ya dauki wannan mataki ne kwanaki kadan bayan Tarayyar Turai ta bukace shi ya yi hakan saboda masu bayar da agaji su iya tara kudin da za a sayi abinci domin kai wa mutanen da ke fama da matsalar ta fari.

Gwamnatin kasar ta ce za ta shigar da masara daga makwabciyarta, wato Zambia.

Dubban dabbobi ne suka mutu a kasar ta Zimbabwe sakamakon rashin abinci.

Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Oxfam da ke Zimbabwe, Jan Vossen, ya shaida wa BBC cewa, "Ruwan saman da yake sauka a wannan shekarar ba shi da yawa, kuma hakan ya sa mutane sun shiga mawuyacin hali."