Kokarin sulhu da Taliban a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto 8am

Wakilai daga kasashe hudu suna taro a karo na uku cikin kasa da wata daya a kokarin samar da wata taswirar zaman lafiya a Afghanistan.

Taliban basu halarci taron ba wanda ke gudana Islamabad tsakanin kasashen Afghanistan da Pakistan da Amurka da kuma China.

Ofishin mataimakin shugaban Afghanistan Abdullah Abdullah yace Kabul ta kagu ta ga an sami sakamako mai ma'ana.

Mai baiwa Pakistan shawara kan harkokin waje Sartaj Aziz yace wajibi ne a yi kokarin shawo kan kungiyoyin Taliban su shiga tattaunawar sulhun.