Sojojin Somalia sun fattaki Al Shabab

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Somaliya a yayin da suke gudanar da wani aiki a Mogadishu, babban birnin kasar.

Sojoji a Somaliya sun ce sun sake kame garin Marka wanda ke bakin gaba, da ke kusa da babban birnin Mogadishu.

Sojojin sun ce sun fattaki 'yan kungiyar Al Shabab ne masu da awar musulunci, kuma masu dauke da makamai, wadanda suka kwace garin a ranar Juma a.

Rahotanni na ambaton mazauna garin na cewa, sojojin Somaliya tare da hadin gwiwar rundunar sojojin Tarayyar Africa a cikin motoci masu sulke, sun sake shiga Marka kwana guda bayan da suka janye.

Sannan suka kara da cewa, fadace-fadace a garin bai yi tsanani ba.

Masu bayar da rahotanni na cewa, wannan shine yunkuri mafi girma da Al Shabab ta yi na kame wurin da ke kusa da babban birnin kasar a cikin watanni.

A 'yan kwanakin nan, kungiyar ta soma kai harin sari-ka-noke, a wani sabon salo na irin yadda ta ke kai hare-harenta.