An bukaci Turkiyya da ta karbi 'yan Syria

Hakkin mallakar hoto Getty

Manyan 'yan siyasar Tarayyar Turai sun yi kira ga gwamnatin Turkiyya da ta karbi dubban 'yan gudun hijirar Syria, da suka isa kan iyaka a kwanaki biyun da suka gabata.

Babbar jami'ar Tarayyar Turai akan manufofin kasashen waje Federica Mogherini ta ce ya kamata a baiwa 'yan gudun hijirar kariya.

Isarsu kan iyakar, ya biyo bayan farmakin da sojojin Syriar suke kaiwa- tare da goyan bayan hare- haren sama na Rasha- akan 'yan tawaye kusa da birnin Aleppo.

Jami'an Turkiyya sunce ana baiwa 'yan gudun hijirar abinci da matsuguni a cikin yankin Syria, kuma akwai bukatar a basu damar tsallakawa cikin Turkiyyan