Tunusia ta katange iyakar ta da Libya

Shugaba Essebsi na Tunusia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tunusia ta dauki matakin ne dan magance matsalar tsaro a iyakar ta da Libya.

Tunisia ta ce ta kammala bangare na farko na aikin gina wani shinge mai tsawon kilomita 200 akan iyakar kasar da Libya, wanda aka tsara domin dakile ta'addanci.

Ministan Tsaron Tunisia ya ce kashi na biyu na aikin zai kunshi makalawa shingen wayar lantarki tare da taimakon gwamnatocin Jamus da kuma Amurka

An dai sanar da gina shingen na a bara, bayan da 'yan bindigar da ake tunanin sun sami horo ne a Libya suka kashe mutane 38 a bakin teku.