Masallatan Biritaniya za su wayar da kan al'umma

Masallatai fiye da tamanin a Biritaniya za su bude kofofinsu ga wadanda ba musulmi ba a yau, domin kokarin wayar musu da kai game da yadda suke daukar addinin na Islama

Musulmin Burtaniyan ne dai suka shirya wannan Taro, saboda damuwa da manyan hare- haren da ake kaiwa da sunan addinin Islama, wanda ke sa mutane da dama tsoron addinin musuluncin

Masallatan za su yi wa jama'a tayin shiga addinin Islama, sannan za kuma su bayarda damar yin sallah, ko kuma mutum ya sha shayi kawai ya tafi