'Kananan hukumomi uku na hannun Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari ya ce babu karamar hukuma ko da guda daya a hannun 'yan Boko Haram.

A Najeriya, wasu 'yan jihar Borno sun ce akwai sauran kananan hukumomi uku karkashin ikon Boko Haram, sabanin abin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ce.

Mutanen sun bukaci Shugaba Buhari ya sake tantance bayanan da yake samu daga dakarun kasar kan kwato yankuna daga hannun Boko Haram.

Wadannan al'umomin na mayar da martani ne dangane da furucin da Buharin ya yi a wata hirar da BBC a karshen mako, inda ya ce babu wata karamar hukuma a kasar da ke hannun mayakan.

Wani dan asalin jihar Bornon ya gaya wa BBC cewa akwai karamar hukumar Mobbar mai hedikwata a Damasak, da karamar hukumar Abadam mai hedikwata a Malamfatori, sai kuma karamar hukumar Guzamala, inda ya ce 'yan kungiyar ta Boko Haram na cin karensu babu babbaka.

Amma wani babban jami'in soji wanda bai yarda a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, duk da cewa ba za a rasa mayakan Boko Haram ba, amma babu wata karamar hukuma da ke karkashin ikonsu a jihar ta Borno.

Ga dai abin da dan asalin jihar Bornon, wanda ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa BBC

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti