Lassa: Ana sanya ido kan mutane 20 a Kano

Image caption Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin kawar da Lassa.

Hukumomin lafiya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ce suna sa ido a kan mutane 20, da ake zato sun yi mu'amala da wani mutum da ya mutu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a makon jiya a jihar.

Hukumomin sun ce mutumin ya je jihar ne daga jihar Benue, ya kuma mutu a lokacin da yake karbar magani a cibiyar ko-ta-kwana da aka tanada a jihar tun bayan da aka samu wanda ya kamu da cutar ta Lassa a wannan karon.

Sun da cewa mutane uku ne suka mutu da cutar ta Lassa a jihar, yayin da mutane sha takwas ne suka nuna alamun kamuwa da cutar a jihar.

Dr. Imam Wada, shi ne mukaddashin mai kula da sashen cutukan al'umma a ma'aikatar lafiya ta Kano, kuma ya yi wa wakilinmu, Yusuf Ibrahim Yakasai, karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ya kara da cewa mutane uku ne suka mutu da cutar ta Lassa a jihar, yayin da mutane sha takwas ne suka nuna alamun kamuwa da cutar a jihar.

A Najeriya, an tabbatar da cewa mutane 72 suka kamu, wanda mutun 45 daga ciki suka rasu.

Jihohi ashirin ne dai a Najeriyar aka bayar da rahoton cewa annobar ta cutar zazzabin Lassa ta shafa.

Wani nau'in farin bera ne dai aka bayyana ke yada kwayar cutar ta Lassa.