An sako matar da aka yi garkuwa da ita a Nijar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban kasar Nijar muhammadou Issofou ya taimaka wajen belin matar da aka yi garkuwa ita 'yar kasar Australia

A Jamhuriyar Nijar, wasu 'yan kishin islama sun sako wata mata 'yar asalin kasar Australia da suka yi awon gaba da ita a watan Janairun da ya gabata.

'Yan kishin Islaman na kungiyar AQMI sun kama ta ne a wani gari mai suna Jibo da ke arewacin Burkina Faso tare da mijinta.

Rahotanni dai na cewa shugaban kasar ta Nijar Alh.Muhammadou Issofou ne ya taimaka wajen samun belin matar Joseline Elliote 'yar asalin kasar Australia.

Fadar shugaban kasar ta ce shugaba Issofou ya yi aiki ne tare da hukumar leken asirin Burkina Faso har ya samu nasarar belin matar 'yar kimanin shekaru tamanin da haihuwa.

Sai dai har yanzu mijin nata na hannun 'yan kishin islaman duk da kiraye-kirayen da iyalansa suka yi.