An kama 'yan kungiyar IS 7 a Spain

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan kungiyar IS

Ministan cikin gidan Spain Jorge Fernandez Diaz yace kama wani gungu na mutane bakwai 'yan kungiyar IS da aka yi a kasar babbar nakasu ce ga kungiyar masu ikirarin jihadin.

Wadanda aka kama din an yi imanin su na jigilar samar da kayayyaki ga mayaka a Syria da Iraqi da suka hada da kudi da bindigogi da kayyakin kwamfuta da kuma abubuwa masu fashewa suna fakewa da cewa kayayyaki ne na taimakon jin kai.

Tun da farko 'yan sanda sun ce yan kungiyar IS sau da dama sun bukaci mutanen da ake zargi su tura musu mata da mayakan su za su aura.

Galibin wadanda aka kama din yan kasar Spain ne kuma dukkaninsu suna da asali da gabas ta tsakiya.