Kwamitin sulhu ya soki Koriya ta Arewa

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da Koriya ta Arewa kan harba roka mai dogon-zango da ta yi.

Kwamitin ya sanar da haka ne bayan tattaunawar gaggawa da mambobinsa su ka yi a New York.

Shugaban kwamitin Rafael Ramirez, wanda shine jakadan Venezuela, ya ce za su amince da kudurin sanya wa Koriya ta Arewar takunkumi akan abin da ya kira abin muni mai hadari da Pyongyang ta yi na karya kudurorin majalisar.

Tun da farko dai hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewan na shirin yin gwajin makamin nukiliya ne a karo na biyar.

Ta ce Koriya ta Arewar na wannan shirin ne bayan da ta harba roka mai nisan-zango -- lamarin da ya saba wa kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.

Koriya ta Arewan ta ce ta yi nasarar harba roka a sararin samaniya, amma masu adawa da ita sun ce tana shirin yin gwajin makamin nukiliya ne.

Makwabtanta da kasashen Yamma sun yi suka sosai akan harba rokar, koda yake dai China da farko ta bayyana rashin jin dadi ne kawai.