'Za a dauki matakai a kan harin Zamfara'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin maharan sun je kauyen ne a kan babura da tsakar dare a lokacin da mutanen kauyen ke barci, sannan suka bude musu wuta da bindigogi

Gwamnatin Nigeria ta bayyana takaicin ta game da asarar rayuka da aka samu a hare-haren da wasu da ake zaton masu satar shanu ne suka kai a jihar Zamfara.

A karshen mako ne dai wasu 'yan bindiga suka kai hari a kauyen Kwana da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutane 23.

Yanzu haka dai mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yomi Osinbanjo, ya dauki matakai don sanin takamaimen halin da ake ciki, kuma nan ba da jimawa ba za a ji irin matakan da suke dauka.

Mutane 23 ne aka tabbatar da mutuwarsu a harin da 'yan bindiga suka kai kan kauyen.

Wani jami'i a yankin ya ce an yi jana'izar mamatan, yayin da mutum guda da ya samu rauni ke jinya a asibiti.

Maharan sun afkawa kauyen ne a daren Asabar, a lokacin da mazauna kauyen ke barci.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin karamar hukumar Maru a majalisar wakilan Najeriya ya shaida wa BBC cewa maharan ba su fuskanci wata turjiya ba a yayin harin, kasancewar babu jami'an tsaro a yankin.

Abdulmalik Zubairu ya zargi gwamnatin kasar da rashin bai wa matsalar tsaro a yankin kulawar da ta kamata.

A shekarar da ta wuce gwamnatin kasar ta kafa wata runduna ta musamman domin yaki da masu satar shanu a jihohin arewacin kasar da aka fi sani da 'Operation sharar daji'.