Bayanai masu karo da juna kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kona garuruwa da dama.

Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya, Kashim Shettima, ya ce babu wata karamar hukuma a jihar da ke hannun Boko Haram.

Gwaman ya bayyana haka ne bayan wasu rahotanni sun ambato wani dan majalisar dattawa daga jihar da kuma wasu mazauna jihar na cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram suna rike da wasu kananan hukumomi.

Wannan lamari dai ya tayar da jijiyoyin wuya, musamman bayan ikirarin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi a kwanakin baya cewa gwamnatinsa ta murkushe kungiyar ta Boko Haram, yadda ba za ta iya kwace garuruwa daga hannun sojoji kamar yadda ta yi a wasu lokuta na baya ba.

Gwamna Shettima ya shaida wa BBC cewa an samu matukar ci gaba a yakin da ake yi da kungiyar ta Boko Haram, yana mai cewa ko da ya ke ya yarda 'yan kungiyar suna rike da wasu yankuna a wasu kananan hukumomin, amma ba sa rike da wata karamar hukuma kacokan.

Ya ce, "A iyaka sani na babu karamar hukuma daya da ke hannu 'yan Boko Haram, amma 'yan kungiyar suna nan jefi-jefi a cikin jeji. Inda ma zan ce suna das karfi shi ne watakila a kananan hukumomin Abadam, da Mabar da Kalabalge. A can din ma ba wai sun rike kananan hukumomin ba ne, suna warwatse a yankunansu".

Ku saurari cikakkiyar hirar da Gwamna Shettima ya yi da BBC

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti