Arangamar yansanda da masu zanga-zanga a Japan

Zanga=zanga a Hong Kong Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zanga=zanga a Hong Kong

Yansanda a Hong Kong sun yi amfani da kulake da hayaki mai sa hawaye lokacin wata arangama da masu zanga-zanga, bayan da suka yi yunkurin hana ciniki a bakin hanya a yankin Mong Kok.

Masu zanga-zangar sun yi ta jifan 'yansandan da duwatsu da sauran tarkace tare da banka wuta a kan titi.

Rundunar Yansanda ta ce ta cafke mutane ashirin da hudu, yayinda aka jikkata jami'anta 48.

Wannan shine tashin hankali mafi muni da aka taba samu tun bayan zanga-zangar nuna goyon bayan dimokaradiiya da aka gudanar a shekara ta 2014.