Shugaba Merkel ta gana da Erdogan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban 'yan gudun hijirar Syria ne ke zaune a kasar Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta fara wata ziyar aiki a kasar Turkiyya, domin tattauna batun rage yawan 'yan gudun hijirar da ke kwarara cikin nahiyar Turai.

Angelar dai ta goyi bayan alkawarin da kungiyar tarayyar Turai ta yi, na bai wa Turkiyya fiye da dala biliyan uku, domin karfafa bakin iyakarta.

Miliyoyin 'yan gudun hijirar Syria ne ke zaune a Turkiyyar, yayin da wasu sama da dubu 35 da suka tserewa rikicin na Syria a kwanakin nan ke naman shiga Turkiyyar.

Wakilin BBC da ke bakin iyakar Turkiyya ya ce kasar ta samu kanta cikin tsaka mai wuya, yayin da tarayyar Turai ke son Turkiyyar ta karbi karin 'yan gudun hijira, a waje daya kuma tana so kasar ta rage yawan 'yan gudun hijirar da ke kwarara cikin kasashen Turai.